SHUGABA TINUBU yaki amincewa da sauya shekar gwamnan kano ba tare da kwankwaso ba
Da ɗumi-ɗumi: Tinubu ya ƙi Amincewq da karɓar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa APC sai tare da Kwankwaso — Uzodinma ya shiga tsakani
Rahotanni daga DAILY NIGERIAN sun nuna cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya fara nuna ƙin amincewa da karɓar sauyin sheƙar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, zuwa jam’iyyar APC, muddin ba tare da uban gidansa na siyasa Sen Rabiu Musa Kwankwaso ba.
Wata majiya ta bayyana cewa shugaban ƙasar ya nace ne saboda irin gagarumin tasiri da Kwankwaso ke da shi a Kano da wasu sassan Arewa.
Sai dai bayan yunƙurin shawo kan Kwankwaso ya ci tura, Hope Uzodinma ya shiga tsakani tare da shawo kan Shugaban ƙasa ya karɓi sauyin sheƙar gwamnan Kano shi kaɗai.
Bisa umarnin gwamna, dukkan ƙungiyoyin shugabannin ƙananan hukumomi a jihar sun yi yunƙurin ƙarshe na roƙon Kwankwaso da ya biyo su APC, inda suka nuna goyon baya ga gwamna tare da kiran sa ya jagorance su zuwa jam’iyyar mai mulki.
Sai dai rabuwar da gwamnan ya yi da jagoransa na tsawon lokaci, Rabiu Kwankwaso, ta tayar da ƙura a cikin sansanin Kwankwasiyya.
Mabiya tafiyar sun fito fili suna caccakar gwamnan tare da jaddada cewa biyayyarsu na nan daram ga Kwankwaso.
A takaice: Rikicin siyasar Kano ya ƙara ɗaukar zafi — yayin da Abba Yusuf ke fuskantar suka daga al'umma Ya yin da mabiya Kwankwasiyya na ƙara ƙarfi, Siyasa ta fara sauya fuska a Kano.

Comments
Post a Comment