Posts

Showing posts from January, 2026

Regragui Ya Caccaki Kocin Senegal Kan Janye ’Yan Wasa A Wasan Ƙarshe Na AFCOn

Image
 Regragui Ya Caccaki Kocin Senegal Kan Janye ’Yan Wasa A Wasan Ƙarshe Na AFCO N Kocin ƙasar Morocco, Walid Regragui, ya yi kakkausar suka ga takwaransa na Senegal, Pape Thiaw, bayan da ya janye ’yan wasansa daga filin wasa domin nuna rashin amincewa da hukuncin fenariti da alƙalin wasa ya bayar a wasan ƙarshe na gasar AFCON. Lamarin ya faru ne a lokacin da alƙalin wasa ya ba da fenariti da ’yan wasan Senegal suka yi amannar cewa ba daidai ba ne. A sakamakon haka, kocin Senegal ya umarci ’yan wasansa da su fice daga filin wasa a matsayin zanga-zanga, lamarin da ya tayar da kura a duniya kwallon kafa ta Afirka. Da yake martani kan abin da ya faru, Regragui ya bayyana wannan mataki a matsayin “abin kunya”, yana mai cewa hakan bai dace da girman gasar AFCON ba, kuma bai girmama ruhin wasanni da adalci da ake so a kwallon kafa ta Afirka ba. “AFCON babbar gasa ce da ke wakiltar mutuncin Afirka. Abin da ya faru bai kamata ya kasance a irin wannan mataki ba,” in ji Regragui. Ya kara da cew...

Gaskiy Game da Ikirarin Cire N7,500 Daga Kowane N100,000 Da Aka Tura

Image
 Gaskiy Game da Ikirarin Cire N7,500 Daga Kowane N100,000 Da Aka Tura A ‘yan kwanakin nan, mutane da dama sun rika yada wani labari a kafafen sada zumunta da ke cewa: “Daga ranar da sabon umarnin gwamnati ya fara aiki, za a rika cire N7,500 daga kowane N100,000 da aka tura ta banki a matsayin haraji.” Wannan ikirari ya jefa ‘yan Najeriya da dama cikin fargaba. Amma bayan bincike mai zurfi, mun gano cewa wannan labari ba gaskiya ba ne. Ga abin da muka gano dalla-dalla: 1. Babu dokar da ta tanadi cire N7,500 daga N100,000 Binciken da aka yi a kan sabuwar dokar haraji da za ta fara aiki daga 1 ga Janairu, 2026 ya nuna cewa: Babu wani sashe a cikin dokar da ya ce gwamnati za ta rika cire kashi 7.5% (N7,500) daga kowanne N100,000 da aka tura. Wannan ikirari karya ne kuma ba shi da tushe a doka. 2. Abin da ke akwai shi ne harajin hatimi (EMTL) Abin da mutane da dama ke rikicewa da shi shi ne Electronic Money Transfer Levy (EMTL), wato harajin hatimi. Wannan haraji yana nufin ₦50 kacal a ...

GWAMNATIN TINUBU TA BIYA ‘DAN LOBBYN REPUBLICAN DALA MILIYAN 9 DON LALLABA TRUMP

Image
 Rahotanni sun bayyana cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta biya wani fitaccen mai lobbyn jam’iyyar Republican har dala miliyan 9, domin yin katsalandan da kuma lallashin tsohon shugaban Amurka Donald Trump, biyo bayan barazanar da Amurka ke yi na iya kai wasu hare-hare kan Najeriya. Majiyoyi sun ce an dauki wannan mataki ne a matsayin kokarin rage radadin takaddamar diflomasiyya da ke kara tsananta tsakanin kasashen biyu, musamman ganin yadda Trump ke kara yin kakkausar magana kan Najeriya a wasu batutuwa na tsaro da manufofin kasa da kasa. An ruwaito cewa wannan dan lobbyn na Republican yana da kusanci da manyan jiga-jigan siyasar Amurka, kuma ana sa ran zai yi amfani da tasirinsa wajen sauya ra’ayin Trump da kuma hana daukar wasu tsauraran matakai da za su iya illata dangantakar Najeriya da Amurka. Sai dai har yanzu gwamnatin Najeriya ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance da ke tabbatarwa ko karyata wannan rahoto ba. Haka kuma, babu wata bayani kai tsaye daga bangaren T...

Kwankwaso Ya Yi Canjin Matsayi, Ya Ba Wa ‘Yan NNPP Ikon Zabe su Je APC

Image
 Kwankwaso Ya Yi Canjin Matsayi, Ya Ba Wa ‘Yan NNPP Ikon Zabe su Je APC Dr. Rabi’u Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano kuma Dan takarar shugaban ƙasa na New Nigeria Peoples Party (NNPP), ya samu cece-kuce a siyasar Najeriya bayan da ya yi sauyin matsayi dangane da batun sauya sheƙa zuwa All Progressives Congress (APC). A cikin wani ƙanƙanin bidiyo da ya bayyana a kafafen sada zumunta, Kwankwaso ya bayyana cewa ya ba wa duk wanda ke da shirin barin jam’iyyar NNPP ya koma APC ‘damar yin hakan idan suna ganin hakan zai bunƙasa musu damar siyasa. Wannan jawabi ya biyo bayan tsawon jayayya da cece-kuce da aka yi a cikin NNPP akan batun da shirye-shirye na sauya sheƙa, musamman daga ɓangaren Gwamna Abba Kabir Yusuf na Kano.  Kwankwaso ya ce cewa yana son a ba wa ‘yan siyasa damar yin amfani da ‘yancin zabe da kai tsaye domin tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai a cikin al’umma, maimakon ci gaba da rikice-rikice cikin jam’iyya.

Laifi Mai Ban Tsoro: Jami’in DSS Ifeanyi Ya Sace Walida, Ya Lalata Ta Tsawon Shekara Biyu, Ya Tilasta Mata Sauya Addini Har Ta Haihu

Image
 Wani jami’in Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) mai suna Ifeanyi na fuskantar mummunan zargi kan sace wata yarinya mai suna Walida, tare da tilasta mata sauya addini daga Musulunci zuwa Kiristanci, sannan kuma yin mata fyade na tsawon kusan shekaru biyu, abin da ya kai ga ta haifi yaro. Rahotanni sun bayyana cewa Ifeanyi ya sace Walida ne tun tana ƙarama, inda ya killace ta a wani wuri da ba a bayyana ba, yana hana ta hulɗa da iyalanta da al’ummarta. A cewar majiyoyi, an ce ya yi amfani da karfin iko da matsayinsa na jami’in tsaro wajen tsoratarwa da kuma hana ta samun taimako. Haka kuma, ana zargin jami’in da tilasta wa yarinyar sauya addini ba tare da yardarta ba, lamarin da ya janyo martani daga kungiyoyin kare hakkin dan Adam da na addini, wadanda suka bayyana hakan a matsayin cin zarafin hakkin ɗan Adam da karya dokoki na kasa da na kasa da kasa. Bayan bullar lamarin, Hukumar DSS ta tabbatar da kama jami’in, tare da jaddada cewa ba za ta kare duk wani jami’i da aka samu da laifi...

Tinubu Ya Isa Abu Dhabi Domin Halartar Taron ADSW 2026

Image
Tinubu Ya Isa Abu Dhabi Domin Halartar Taron ADSW 2026 Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sauka a birnin Abu Dhabi na Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) a daren Lahadi, domin halartar babban taron duniya na Abu Dhabi Sustainability Week (ADSW) 2026, wanda aka fara yau Litinin. Jirgin Shugaban Ƙasan ya sauka a Sashen Shugaban Ƙasa na Filin Jirgin Sama na Zayed da misalin ƙarfe 11:30 na dare agogon Dubai, inda manyan jami’an gwamnatin UAE da na Najeriya suka tarbe shi. Daga cikin waɗanda suka yi masa maraba akwai Ministan Harkokin Wajen UAE, Sheikh Shakhboot Nahyan Al Nahyan, Jakadan UAE a Najeriya Salem Saeed Al-Shamsi, Ministan Harkokin Wajen Najeriya Amb. Yusuf Maitama Tuggar, tare da jami’an ofishin jakadancin Najeriya da ke Abu Dhabi. Har ila yau, wasu manyan jami’an gwamnatin tarayya sun tarbi Shugaban Ƙasan a otal ɗinsa, ciki har da Ministan Kasafi da Tsare-tsare Atiku Bagudu, Ministan Masana’antu, Ciniki da Zuba Jari Dr. Jumoke Oduwole, da Darakta-Janar na Hukumar Leken Asiri ta Ƙa...

Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Yi Tattaunawa da Kwankwaso, Daga Bisani Ya Tafi Faransa Don Ganawa da Tinubu

Image
 Rahotanni sun nuna cewa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gudanar da wata ganawa ta musamman da jagoran NNPP kuma tsohon gwamnan jihar, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, a gidansa da ke Miller Road a birnin Kano. Majiyoyi sun bayyana cewa ganawar ta gudana ne a ranar Talata, inda aka tattauna muhimman batutuwa da suka shafi siyasa da makomar jam’iyya a jihar Kano da ma kasa baki daya. Bayan wannan ganawa, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tafi kasar Faransa a ranar Juma’a, inda ake sa ran zai gana da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu. Wata majiya ta shaida wa DAILY NIGERIAN cewa tafiyar ta Gwamnan na da nasaba da shawarwari da ake yi a matakin kasa, musamman kan hadin gwiwa da fahimtar juna tsakanin manyan ‘yan siyasa. Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga bangaren Gwamnan Kano, Sanata Kwankwaso ko kuma fadar shugaban kasa dangane da cikakken dalilin ganawar ko tafiyar.

Zamu karbi Greenland koda tsiya tsiya cewar Donald Trump

Image
 Yayin da yake jawabi ga manema labarai a ranar Juma’a, Mista Donald Trump ya bayyana cewa wasu ƙasashe na nuna sha’awar mallakar yankin Greenland, yana mai cewa “dole ne Amurka ta ɗauki matakan kare aukuwar hakan.” A kwanakin baya, Fadar White House ta tabbatar da cewa tana nazarin yiwuwar sayen yankin daga ƙasar Denmark. Sai dai, duk da wannan mataki, ta jaddada cewa har yanzu ba a kawar da yiwuwar amfani da ƙarfin soji domin mamaye yankin ba. Sai dai wannan furuci ya fuskanci martani mai ƙarfi daga Denmark da kuma hukumomin tsibirin Greenland, inda suka bayyana karara cewa yankin ba na sayarwa ba ne, kuma ba za su amince da kowace irin mamaya ba. A halin yanzu, tsibirin Greenland na ci gaba da jan hankalin manyan ƙasashen duniya, sakamakon dumbin albarkatun ma’adinai da ke ɓoye a ƙarƙashin ƙankarar yankin, lamarin da ke ƙara tsananta fafatawar siyasa da tattalin arziki a yankin Arctic.

Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Zuwa Ga Dr. Rabiu Musa Kwankwaso

Image
 Buɗaɗɗiyar Wasiƙa Zuwa Ga Dr. Rabiu Musa Kwankwaso Dear Baba, Jagora, Madugu, Sanata Dr. Rabiu Musa Kwankwaso, Ina rubuto wannan wasiƙa gare ka ba kawai a matsayin ’yar siyasa zuwa ga dattijo ba, amma a matsayin ’ya, almajira, kuma ’yar ƙasa mai kishin ƙasa wadda ke magana da uba mai hangen nesa, jarumtaka, da tasiri. Kai mutum ne da tafiyarka a harkar jama’a ta ba wa mutane da dama fata—musamman waɗanda a da suke ganin dama ba ta tanadar musu ba. Ka tabbatar, ta hanyar aiki ba magana kawai ba, cewa ɗa ko ’yar talaka na iya kaiwa kololuwa ba ta hanyar sadaka ba, sai ta hanyar tsari, ilimi, da gaskatawa. Ka yi doguwar tafiya a hidimar ƙasa: a matsayin ma’aikacin gwamnati, jakada, gwamnan jiha, ɗan majalisa, minista, da bawan jama’a. A duk waɗannan matakai, abu ɗaya ya tsaya daram—ƙudurin ka wajen inganta rayuwar jama’a, musamman ta fannin ilimi da bunƙasa ƙwarewar ɗan Adam, ba abin musantawa ba ne. Ba wai ka yi magana ne kawai kan ɗaga martabar mutane ba; ka gina tsare-tsare da suk...

Alummar garin dadin kowa na cikin firgici a jihar gombe

Image
 Al’ummar garin Daɗin-kowa da ke Ƙaramar Hukumar Yamaltu-Deba a Jihar Gombe na rayuwa ne cikin firgici da halin kashiya, yayin da dorinar ruwa ke ci gaba da cin karenta ba babbaka a Madatsarruwa ta Daɗin-kowa, lamarin da ya zama babbar barazana ga rayuka da tattalin arzikin yankin. A halin da ake ciki, gonaki masu darajar miliyoyin naira sun nutse ƙarƙashin ruwa, amfanin gona ya lalace gaba ɗaya, gidaje sun rushe, yayin da dubban mazauna ke fuskantar barazanar rasa matsuguni. Duk da tsananin wannan iftila’i, al’umma na zargin hukumomi da sakaci da shiru mai kama da watsi da rayukan talakawa. Masu sana’ar kamun kifi – wadda ita ce ginshiƙin rayuwar yankin – sun shiga mawuyacin hali, bayan da ruwan ya tarwatsa hanyoyin kamun kifi, ya hallaka kifaye, tare da toshe hanyoyin samun abin dogaro. Wannan ya jefa iyalai da dama cikin yunwa da fatara, yayin da wasu ke fargabar barkewar cututtuka sakamakon gurbacewar ruwan sha. Rahotanni daga cikin gari sun tabbatar da cewa an riga an samu asa...

Atiku da tambuwal ne suka lalata PDP

Image
 Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya bayyana cewa duk da kasancewarsa jigo kuma mai biyayya ga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya kasance mai gaskiya da rikon amana game da matsayinsa na siyasa, musamman dangane da zaɓen shugaban ƙasa na 2023. Fayose ya ce bai taɓa ɓoye ra’ayinsa ba lokacin da ya yanke shawarar goyon bayan Bola Ahmed Tinubu, ɗan takarar jam’iyyar All Progressives Congress (APC), duk da cewa jam’iyyarsa ta PDP tana da nata ɗan takara a wancan lokaci. A cewarsa, wannan matsaya tasa ta samo asali ne daga abin da ya kira gaskiya da fahimtar siyasar ƙasa, ba wai cin amanar jam’iyya ba. Ya jaddada cewa siyasa ba wai makanta ba ce, kuma mutum na iya kasancewa ɗan jam’iyya amma har yanzu ya bayyana ra’ayinsa bisa abin da ya yi imani da shi. Fayose ya ce ya yi hakan ne domin yana ganin Tinubu ya fi cancanta a wancan lokaci, musamman ta fuskar kwarewa, dabarun siyasa da kuma fahimtar tafiyar da ƙasa mai rikitarwa kamar Najeriya. Tsohon gwamnan ya ƙara da...

ƊUMI-ƊUMI: Jirgin tsaron gabar tekun Amurka na bin jirgin dakon mai mai tutar Rasha a tekun Atlantika

Image
 Jirgin ruwan tsaron gabar tekun Amurka na ci gaba da bin diddigin wani jirgin dakon man fetur mai dauke da tutar Rasha a yankin arewacin tekun Atlantika, bayan da ake zargin jirgin ya keta shingen tsaro da Amurka ta kafa a yankin. Rahotanni sun bayyana cewa jirgin dakon man na Rasha ne, kuma har yanzu bai tsaya ba duk da kokarin da sojojin ruwan Amurka ke yi na tilasta masa tsayawa. Sai dai sojojin Amurka sun jaddada cewa burinsu shi ne kwace jirgin dakon man, ba wai kai masa hari ko haddasa nutsewarsa ba. Amurka na zargin cewa jirgin yana jigilar man fetur ne daga kasashen Iran da Venezuela, lamarin da ta ce ya saba wa takunkumin tattalin arziki da ta kakabawa kasashen

ƊUMI-ƊUMI: Ana fargabar barkewar sabon rikici a Yemen bayan shugaban STC ya ɓac

Image
 ƊUMI-ƊUMI: Ana fargabar barkewar sabon rikici a Yemen bayan shugaban STC ya ɓac e Ana fargabar barkewar sabon rikici a ƙasar Yemen, bayan rahotanni sun tabbatar da cewa shugaban ƙungiyar Southern Transitional Council (STC), Aidrous al-Zubaidi, ya tsere zuwa wani wuri da ba a bayyana ba. Kawancen ƙasashen da Saudiyya ke jagoranta ya bayyana cewa al-Zubaidi ya ƙi zuwa Saudiyya domin halartar tattaunawar da aka shirya, wadda ke da nufin kawo ƙarshen rikicin siyasa da na tsaro da ya sake ɓarke a wasu sassan ƙasar. Mai magana da yawun kawancen, Janar Turki al-Maliki, ya ce an umurci al-Zubaidi da ya shiga jirgin da aka tanada domin ganawa da shugabannin Yemen, amma bai bayyana ba, duk da cewa wasu manyan jami’an STC sun bi umarnin suka tafi Saudiyya. Bayan kin tafiyar tasa, kawancen ya ce ya gano motsin dakaru da makamai masu nauyi a birnin Aden da kewaye, lamarin da ya haifar da fargabar barkewar rikici tsakanin bangarorin Yemen. Saboda haka, kawancen ya ce ya ɗauki matakan tsaro na g...

Daga Karatu zuwa Soyayya: Labarin Gideon Kirui da Ya Ci Nasara Duk da Ƙalubale

Image
 Daga Karatu zuwa Soyayya: Labarin Gideon Kirui da Ya Ci Nasara Duk da Ƙalubale Gabatarwa Gideon Kirui ya bar ƙasarsa ne da buri ɗaya a zuciya — neman ilimi a ƙasar Isra’ila. Amma kamar yadda rayuwa take cike da abubuwan mamaki, tafiyar tasa ta sauya alkibla lokacin da ya haɗu da soyayyar da ba ya tsammani. Abin da ya fara da burin karatu, ya rikide zuwa labarin ƙauna mai cike da ƙalubale, juriya da nasara. Tafiya zuwa Isra’ila Gideon Kirui ya tafi Isra’ila domin ci gaba da karatunsa, inda ya shiga sabon yanayi, al’adu da mutane daban-daban. A wannan sabon muhalli ne rayuwarsa ta fara ɗaukar wani sabon salo, wanda bai taɓa hango shi a baya ba. Haduwa da Soyayya A yayin zamansa a Isra’ila, Gideon ya haɗu da wacce zuciyarsa ta kamu da ƙauna. Soyayyar ta zo masa ba tare da shiri ba, amma ta girma cikin sauri. Duk da farin cikin da soyayyar ta kawo masa, Gideon ya san cewa hanya a gabansa ba za ta kasance mai sauƙi ba. Ƙalubalen Iyalin Gargajiya Gideon ya fito ne daga gida mai tsattsau...

🇻🇪 Venezuela za ta ba da har zuwa miliyan 50 na gangar mai zuwa Amurka — Trump

Image
 🇻🇪 Venezuela za ta ba da har zuwa miliyan 50 na bariloli zuwa Amurka — Trump Washington / Caracas, 07 Janairu 2026 Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana a ranar Talata cewa gwamnatin rikon kwarya ta Venezuela ta amince za ta mika tsakanin 30 zuwa 50 miliyan bariloli na “sanctioned oil” zuwa Amurka. Trump ya ce wannan mai zai ƙaru kai tsaye zuwa tashoshin jiragen ruwa na Amurka daga tankunan ajiya. � ABC News +1 Ya bayyana cewa za a sayar da wannan mai a farashin kasuwa, kuma kudaden da aka samu daga sayarwar za su kasance kula da su a karkashin ikon shugaban kasa domin a tabbatar ana amfani da su don amfanin “mutanen Venezuela da na Amurka”. Trump ya ce ya ba da umarnin Sakataren Makamashi, Chris Wright, ya aiwatar da shirin nan take. � ABC News +1 Sanarwar ta biyo bayan ƙaddamar da wani babban aiki na soji da Amurka ta jagoranta a Venezuela, inda tsohon shugaban ƙasar Nicolás Maduro da matarsa aka kama, lamarin da ya jawo suka daga hukumomin Caracas da kuma ƙasashen duniya....

Iran Ta Yi Gargaɗi: Ba Ma Ɗaukar Barazana da Wasa, Za Mu Maida Martani Mai Tsanani‼️

Image
Iran Ta Yi Gargaɗi: Ba Ma Ɗaukar Barazana da Wasa, Za Mu Maida Martani Mai Tsanani‼️ 🚨 BREAKING NEWS  Sakatariyar Majalisar Tsaron Iran ta bayyana cewa ƙasar ba ta ɗaukar kowace barazana daga maƙiyanta da wasa. Ta ce Iran a shirye take ta ɗauki tsauraran matakai, tare da mayar da martani mai ban mamaki ga duk wani hari da zai taso. Sakatariyar Majalisar Tsaron Iran ta bayyana cewa ƙasar Iran ba ta ɗaukar kowace irin barazana daga maƙiyanta da wasa. A cewarta, Iran na da cikakken shiri da ƙwarewa wajen kare kanta, inda ta jaddada cewa duk wani hari ko yunƙurin barazana zai fuskanci martani mai tsauri da ba a zata ba. Ta ƙara da cewa matakan tsaron Iran sun kai matakin da zai ba ta damar fuskantar kowanne irin barazana cikin ƙarfi da jarumtaka.

ƊUMI-ƊUMI: Isra’ila Ta Kammala Shirye-shiryen Kai Hari Ƙarƙashin Ƙasa Kan Ira

Image
 ƊUMI-ƊUMI: Isra’ila Ta Kammala Shirye-shiryen Kai Hari Ƙarƙashin Ƙasa Kan Ira n Rahotanni sun bayyana cewa a ranar Litinin da ta gabata, kwamitin tsaron ƙasar Isra’ila ya amince da shirin ƙaddamar da yaki a kan ƙasar Iran, wani yaki da aka sanya wa suna “Operation Iron Strikes.” Majiyoyi sun ce an riga an zaɓi rana da lokacin da za a fara kai harin. Masu nazarin al’amuran tsaro sun yi gargadin cewa idan Isra’ila ta aiwatar da wannan hari, duniya na iya shiga cikin wani mummunan rikici, duba da yadda Iran za ta mayar da martani domin kare kanta. A shirye-shiryen kare kai, Iran ta fara gwaje-gwajen sabbin makaman linzami masu nisan zango (ballistic missiles), tare da ƙarfafa tsarin tsaron ƙasarta. Wannan mataki ya ƙara tayar da hankalin Isra’ila da kawayenta, musamman Amurka. Rahotanni sun nuna cewa Isra’ila da Amurka na fatan rusa tsarin mulkin Iran domin kafa shugabancin da zai yi musu biyayya. A halin yanzu, ana kallon Iran a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashen da Isra’ila ke fi ts...

Yakamata Victor osimehn ya gyaran dabi"arsa

Image
 Victor Osimhen ya kamata ya gyara ɗabi’arsa. Wannan na daga cikin manyan dalilan da suka hana manyan kulob-kulob ɗaukar sa. Ademola Lookman ne ya tallafa masa da ƙwallo har guda biyu, amma duk da haka Osimhen ya nuna wani hali da ya sa ya zama abin magana a idanun duniya. Kamar yadda Osimhen yake babban ɗan wasa, haka ma Lookman babban ɗan wasa ne. Bai dace a raina shi ba kamar ana mu’amala da ɗan wasan NPFL. 😀

Korea ta Arewa ta harba makamai masu linzami

Image
 Koriya ta Arewa ta harba makamai masu linzami na ballistic da dama daga Pyongyang zuwa tekun da ke gabashin ƙasar a ranar Lahadi, a cewar sojojin Koriya ta Kudu. Wannan harba makamai shi ne na farko cikin watanni biyu, kuma shi ne na farko a sabuwar shekarar nan. Gwajin ya faru ne sa’o’i kaɗan kafin ziyarar Shugaban Koriya ta Kudu, Lee Jae Myung, zuwa China domin halartar wani taron ƙoli. Shin me za ku ce game da wannan?

Fir’auna Netanyahu” – Erdogan Ya Zargi Isra’ila da Zaluntar Fararen Hula a Gaza

Image
 “Fir’auna Netanyahu” – Erdogan Ya Zargi Isra’ila da Zaluntar Fararen Hula a Gaza Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdoğan, ya jefa kalaman da suka girgiza duniya a ranar Juma’a yayin wata hira da ‘yan jarida a birnin Ankara. Ya kira Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, da “fir’auna”, yana mai zargi da jawo mutuwar dubban fararen hula a Gaza, daga yara ‘yan shekara bakwai har zuwa tsofaffi masu shekaru saba’in. Erdogan ya jaddada cewa tarihin zalunci ba ya gushewa ba tare da hukunci ba, yana mai kira ga al’ummar duniya da su ɗauki matakin adalci kan abin da ke faruwa a yankin. Shugaban na Turkiyya ya bayyana cewa shiru ko jinkirin daukar mataki daga ƙasashen duniya na iya zama gudummawa ga ci gaba da take haƙƙin bil’adama. Masu sharhi kan siyasar duniya sun ce irin wannan furuci na Erdogan na iya ƙara matsin lamba ga Isra’ila, musamman ta fuskar ra’ayin jama’a da kuma ƙarfafa kira ga hukumomi da su duba halin da ake ciki a Gaza.

Ruben Amorim ya samu korar aiki a Manchester United — a yau!

Image
🔴 Ruben Amorim ya samu korar aiki a Manchester United — a yau! 🌍 Labarin daga kafofin wasanni na duniya ya nuna cewa Ruben Amorim, babban manager/head coach na Manchester United, an kore shi daga aikin bayan watanni masu rikitarwa a Old Trafford. � The Sun 📉 Me ya faru? Amorim, wanda ya hau kujera tun Nuwamba 2024, ya fuskanci matsin lamba saboda sakamako marasa kyau da rashin kyakkyawar nasara a wasannin Premier League da sauran gasar. � The Sun An ce rikici ya kara tsananta lokacin da ya yi sokaci ga shugabannin kulob a bainar jama’a game da rashin goyon bayan da yake ji – musamman kan manufofin canje-canjen ‘yan wasa da tsarin aiki. � The Sun A wannan matakin, kulob din ya yanke shawarar raba hanya da shi da nan take. � The Sun 👔 Menene hakan yake nufi? Wannan yana nufin cewa Amorim ba zai ci gaba da jagorantar Manchester United ba kuma kulob zai fara neman sabon manajan guda. � The Sun A halin yanzu, ana tsammanin Darren Fletcher zai shiga matsayin interim boss (na wucin gadi) ...

Me yasa sauya shekar gwamnan kano ke tayar da kura

Image
 Me ya sa sauyin shekar Gwamnan Kano ke tayar da kura a fadin kasa? Duk da cewa a ‘yan kwanakin nan an sha ganin gwamnoni suna sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki, sauyin shekar Gwamnan Kano ya dauki hankalin jama’a fiye da na sauran jihohi, tare da tayar da muhawara a fadin Najeriya. Masana siyasa na danganta hakan da muhimmancin Kano a taswirar siyasar kasa. Kano jiha ce da ke da yawan jama’a da kuri’u masu yawa, lamarin da ke sa duk wani canjin siyasa a cikinta ya wuce matakin jiha zuwa matakin kasa. Duk jam’iyyar da ta samu karfi a Kano na kara samun karbuwa a Arewa da ma Najeriya baki daya. Wani muhimmin dalili kuma shi ne asalin tafiyar siyasar gwamnan, wanda ya fito daga tafiyar Kwankwasiyya. Wannan tafiya na da karfi sosai, tare da mabiyan da ke da tsayayyen ra’ayi. Saboda haka, sauyin sheka daga wannan tafiya zuwa jam’iyya mai mulki na dauke da sakonni masu zurfi ga ‘yan siyasa da jama’a. Bugu da kari, Kano ta kasance daya daga cikin manyan ginshikan adawa a zaben da ya ga...

Kasar Amurka Ta Kama Shugaban Kasar Panama Manuel Noriega

Image
 Kasar Amurka Ta Kama Shugaban Kasar Panama Manuel Noriega  A ranar 3 ga Janairu 1990 (yau Shekaru 36 da suka wuce) Manuel Noriega, shugaban kasar  Panama, ya mika wuya ga hukumomin Amurka. Kama shi shi ne babban manufar (Operation Just Cause), wata mamayar Amurka mai girma da aka ƙaddamar a kasar a ranar 20 ga Disamba, 1989.  Mamaya bayan hare-haren Jiragen Saman Yaki Bayan mamayar da sojojin Amurka kimanin 24,000 suka yi, Noriega ya kauce wa kamawa na tsawon kwanaki da dama. Mafaka a Ofishin Jakadancin Vatican A ranar Kirsimeti, 1989, Noriega ya nemi mafaka a cikin (ofishin jakadancin Vatican) a birnin Panama. Domin tilasta masa fita ba tare da karya ka'idojin diflomasiyya ta hanyar shiga ofishin jakadancin ba, sojojin Amurka sun yi amfani wakokin rock da manyan mayan sufiku masu azabar ƙarfi, suka kewaye ofishin jakadancin suka kunna kida ba dare ba rana. Wasu daga cikin wakokin da suka kunna sun hada da: Panama" ta Van Halen "Welcome to the Jungle" ta Guns N'...

SHUGABA TINUBU yaki amincewa da sauya shekar gwamnan kano ba tare da kwankwaso ba

Image
 Da ɗumi-ɗumi: Tinubu ya ƙi Amincewq da karɓar Gwamna Abba Kabir Yusuf zuwa  APC sai tare da Kwankwaso — Uzodinma ya shiga tsakani Rahotanni daga DAILY NIGERIAN sun nuna cewa Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya fara nuna ƙin amincewa da karɓar sauyin sheƙar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, zuwa jam’iyyar APC, muddin ba tare da uban gidansa na siyasa Sen Rabiu Musa Kwankwaso ba. Wata majiya ta bayyana cewa shugaban ƙasar ya nace ne saboda irin gagarumin tasiri da Kwankwaso ke da shi a Kano da wasu sassan Arewa.  Sai dai bayan yunƙurin shawo kan Kwankwaso ya ci tura, Hope Uzodinma ya shiga tsakani tare da shawo kan Shugaban ƙasa ya karɓi sauyin sheƙar gwamnan Kano shi kaɗai. Bisa umarnin gwamna, dukkan ƙungiyoyin shugabannin ƙananan hukumomi a jihar sun yi yunƙurin ƙarshe na roƙon Kwankwaso da ya biyo su APC, inda suka nuna goyon baya ga gwamna tare da kiran sa ya jagorance su zuwa jam’iyyar mai mulki. Sai dai rabuwar da gwamnan ya yi da jagoransa na tsawon lokaci, Rabiu Kwan...

Aina matsalar take akan Yan wasan kwaykwayo na Arewacin Nigeria

 

Shirin Komawa APC: Tijjani Gandu Ya Aika Saƙo Mai Zafi Ga Gwamna Abba Gida-Gida

Image
 Shirin Komawa APC: Tijjani Gandu Ya Aika Saƙo Mai Zafi Ga Gwamna Abba Gida-Gida Ƙungiyar mawallafan Kwankwasiyya da ke rera wakoki tare da nuna goyon baya ga ƙungiyar Kwankwasiyya da jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ta yi kira ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya sasanta da Sanata Kwankwaso domin cimma matsaya guda kan makomar magoya bayansu. Shugaban ƙungiyar mawallafan, kuma fitaccen mawakin Kwankwasiyya da gwamnatin Abba, Tijjani Gandu, ne ya bayyana hakan a wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis. A cewar Tijjani Gandu, sun zaɓi yin bidiyon ne saboda rashin samun damar ganawa kai tsaye da Gwamna Abba Kabir Yusuf. Ya bayyana cewa mawakan Kwankwasiyya na da buƙatar gwamnan ya nemi Sanata Kwankwaso domin su zauna su tattauna, ganin irin doguwar alaƙar siyasa da ke tsakaninsu wadda ta shafe kusan shekaru 40. Ya ƙara da cewa, a matsayinsu na waɗanda suka taka rawar gani wajen kafa gwamnatin Abba Kabir Yusuf, sun...

Tsohon Shugaban Sudan Ya Zargi CIA da Kirkirar Boko Haram da ISIS

Image
 Tsohon Shugaban Sudan Ya Zargi CIA da Kirkirar Boko Haram da ISIS Tsohon shugaban ƙasar Sudan, Omar Hassan al-Bashir, ya taɓa fitowa fili yana zargin hukumar leƙen asirin Amurka (CIA) da kuma Mossad ta Isra’ila da cewa su ne ke da hannu a ƙirƙira ko tallafa wa ƙungiyoyin ta’addanci irin su Boko Haram da ISIS. Al-Bashir ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da kafafen yaɗa labarai na ƙetare a shekarun baya, inda ya ce ayyukan da waɗannan ƙungiyoyi ke aikatawa ba za a iya danganta su da Musulunci na gaskiya ba. A cewarsa, hakan ya sa yake da ra’ayin cewa akwai hannun manyan hukumomin leƙen asiri na ƙasashen yamma a bayan kafuwar ƙungiyoyin. Ya ƙara da cewa manufar hakan ita ce ɓata sunan Musulunci, tayar da rikici a ƙasashen Afirka da Gabas ta Tsakiya, tare da ba wa wasu ƙasashe damar tsoma baki cikin harkokin cikin gida na ƙasashen da abin ya shafa. Ra’ayin Masana da Gaskiyar Lamarin Duk da wannan zargi mai nauyi da tsohon shugaban Sudan ya yi, masana harkokin tsaro da binciken ...

Rundunar ƴansandan kasar nan ta sanar da dakatar da kamen motoci masu gilashi mai duhu a faɗin ƙasar, biyo bayan umarnin kotu na wucin-gadi.

Image
 Rundunar ƴansandan kasar nan ta sanar da dakatar da kamen motoci masu gilashi mai duhu a faɗin ƙasar, biyo bayan umarnin kotu na wucin-gadi. A sanarwar da ta fitar a shafinta na X, rundunar ta ce matakin dakatarwar ya biyo bayan ƙarar da ke gaban kotu, inda aka umurci rundunar ta dakata daga aiwatar da dokar, har sai an yanke hukunci. Tun a ranar 15 ga Disamba, 2025 ne rundunar ta bayyana aniyarta ta fara aiwatar da dokar mallakar lasisin amfani da gilashin mota mai duhu daga ranar 2 ga Janairu, 2026, tana mai cewa hakan na da nufin ƙarfafa tsaro da kare lafiyar jama’a.

Anyi garkuwa da sarki a nasarawa state Nigeria

Image
 An yi garkuwa da Basarake Aniwo na 1 na al’ummar Aafin, da ke gundumar Ile-Ire a Ƙaramar Hukumar Ifelodun ta Jihar Kwara, wato Oba Simeon Olaonipekun, tare da ɗaya daga cikin ’ya’yansa mai suna Olaolu, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin firgici da tashin hankali. Rahotanni sun bayyana cewa masu garkuwar sun kai harin ne a wani lokaci da ba a bayyana ba, inda suka afka gidan basaraken ko kuma suka tare su a hanya (gwargwadon bayanan farko), sannan suka tafi da su zuwa wani wuri da ba a sani ba. Har zuwa yanzu, ba a tabbatar da inda aka kai su ba. Bayan faruwar lamarin, jami’an tsaro sun fara gudanar da bincike tare da kai samame a wasu yankuna domin ceto basaraken da ɗansa. Haka kuma, shugabannin al’umma da mazauna yankin sun yi kira ga hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen ganin an kubutar da su cikin koshin lafiya. Al’ummar Aafin sun bayyana damuwarsu matuƙa, inda suka bayyana sace basarake a matsayin babban hari ga zaman lafiya da martabar masarautar gargajiya. Wasu daga ...

DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnan Filato Caleb Mutfwang Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP

Image
 DA ƊUMI-ƊUMI: Gwamnan Filato Caleb Mutfwang Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP Rahotanni daga jihar Filato sun tabbatar da cewa Gwamna Caleb Mutfwang ya ajiye membobinsa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), sai dai har yanzu ba a bayyana sabuwar jam’iyyar da zai koma ba.

Chelsea Ta Sallami Manajan Su, Enzo Maresca: Me Ya Faru?

Image
 Ranar 1 ga Janairu 2026 ta kasance mai ɗan girgiza a Stamford Bridge, yayin da Chelsea Football Club ta sanar da sallamar manajan ta, Enzo Maresca. Wannan lamari ya zo ne a lokacin da ƙungiyar ke fuskantar matsin lamba a gasar Premier League, inda ta yi nasara sau ɗaya kacal cikin wasanni bakwai da suka gabata. Dalilin Sallama Rahotanni sun bayyana cewa rashin nasarori da rashin jituwa tsakanin Maresca da shugabannin kulob sun taka rawa wajen yanke wannan hukunci. Duk da cewa Maresca ya samu nasarori a baya, ciki har da lashe UEFA Conference League da FIFA Club World Cup, rashin kyakkyawan sakamako a gasar gida ya sa kulob ɗin yanke shawarar canza manaja. Chelsea ta bayyana cewa wannan mataki zai taimaka wa ƙungiyar ta komawa cikin sahun manyan kungiyoyi kuma ta gyara sakamakon wasannin lig. Tasirin Sallama Sallamar Maresca ba kawai canji a kan titin kulob ba ne, har ma tana nuna cewa Stamford Bridge na neman sabon shugaba mai jagorantar ƙungiyar cikin nasara. A halin yanzu, kulob...

SHUGABA TINUBU YASHA ALWASHIN MURKUSHE DUK WATA BARZANA A 2026

Image
 Na Sha Alwashin Zurfafa Haɗin Gwiwa Da Kasashen Duniya Domin Murƙushe Barazanar Tsaro A 2026, Inji Shugaba Tinubu Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta ƙara zurfafa haɗin gwiwa da ƙasashen yankin da na duniya a shekarar 2026, domin kawar da dukkan barazanar tsaro da ke barazana ga rayuka, dukiyoyi da kuma cikakken ikon ƙasar Najeriya. Shugaban ya bayyana hakan ne a jawabin saƙon sabuwar shekarar 2026 da ya gabatar ga ’yan Najeriya a ranar Alhamis. Tinubu ya ce tafarkin gyara ƙasar na ba abu ne mai sauƙi ba, amma wajibi ne, yana mai jaddada cewa ci gaban tattalin arziki ba zai yi armashi ba tare da tsaro da zaman lafiya ba. Ya ce Najeriya na ci gaba da fuskantar barazanar ’yan ta’adda da masu aikata laifuka da ke ƙoƙarin dagula zaman lafiyar ƙasa, amma gwamnati na ɗaukar matakan da suka dace domin dakile su. Shugaban ya bayyana wasu hare-hare da aka kai kwanan nan tare da haɗin gwiwar abokan hulɗa na ƙasa da ƙasa, ciki har da Amurka, domin raunana ƙungiy...

Yan Ta’adda Sun Kashe Mutum 7 a Sabon Hari a Filato

Image
 Aƙalla mutane bakwai ne suka rasa rayukansu sakamakon wani sabon harin dare da wasu ‘yan ta’adda suka kai a garin Bum, da ke cikin ƙaramar hukumar Vwang (Vwamg) a Jihar Filato. Rahotanni sun nuna cewa maharan sun shiga garin ne cikin dare, inda suka rika harbe-harbe ba kakkautawa, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin fargaba da tashin hankali. Mutanen da abin ya shafa sun hada da mazauna garin da ba su ji ba su gani ba. Wasu mazauna yankin sun ce bayan harin, an gano gawarwakin mutane bakwai, yayin da ake fargabar cewa adadin na iya ƙaruwa saboda wasu sun jikkata kuma ana ci gaba da neman wasu da suka bace. Har zuwa lokacin hada wannan labari, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba, sai dai an ce an tura jami’an tsaro zuwa yankin domin dawo da zaman lafiya da kuma gudanar da bincike. Al’ummar garin Bum sun bukaci gwamnati da hukumomin tsaro da su dauki matakan gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a, ganin yadda hare-haren ke kara yawaita a wasu sassa...

Tattalin arzikin Nigeria ya karu

Image
 Tattalin Arziƙin Nijeriya Ya Kara Karfi A Watan Disamba, Yayin Da Malejin Hadahadar Kamfanoni Da Masana'antu Ya Kai Maki 57.6 – CBN Daga Ashafa Murnai Barkiya Babban Bankin Najeriya (CBN) ya bayyana cewa  saɓatta-juyattar ayyukan tattalin arziƙin cikin gida sun ci gaba da ƙarfafa a watan Disamba 2025, yayin da malejin ƙarfin hadahadar masana'antu, wato 'Composite Purchasing Managers’ Index' (PMI) ya ci gaba da kasancewa sama da maki 50.  Hakan dai kenan ya nuna irin yadda ake samun faɗaɗar ayyukan tattalin arziƙi. Rahoton binciken PMI na watan Disamba 2025 da Babban Bankin ya fitar ya nuna cewa ƙarfin PMI ya kai maki 57.6, wanda ke tabbatar da samun bunƙasar tattalin arziki mafi ƙarfi da aka samu a kusan shekaru biyar da suka gabata. Rahoton ya ce wannan ci gaba mai ɗorewa ya samo asali ne daga faɗaɗa ayyuka a manyan sassa da ke samar da ayyukan yi. “Sakamakon PMI na ɓangarori ya nuna cewa harkokin noma da ayyukan gona ya ci gaba da ƙarfi da maki 58.5, masana’antu sun ...

Allah Ya Yi Wa Sanatan Nasarawa, Godiya Akwashiki Rasu

Image
 Rahotanni sun tabbatar da rasuwar Sanata Godiya Akwashiki, wanda ke wakiltar Nasarawa North Senatorial District a Majalisar Dattawan Najeriya. Sanatan ya rasu ne a ranar 31 ga Disamba, 2025, a wani asibiti da ke ƙasar Indiya, bayan ya shafe lokaci yana fama da doguwar rashin lafiya. 👤 Tarihinsa a taƙaice Marigayi Godiya Akwashiki an haife shi ne a ranar 3 ga Agusta, 1973, a ƙaramar hukumar Nasarawa Eggon, Jihar Nasarawa. Kafin zamansa sanata, Akwashiki ya rike muƙamai daban-daban a Majalisar Dokokin Jihar Nasarawa, inda ya taba zama: Majority Leader Mataimakin Kakakin Majalisa (Deputy Speaker) 🏛️ Aikinsa a Majalisar Dattawa Akwashiki ya shiga Majalisar Dattawa ne a shekarar 2019, kuma aka sake zabar sa a 2023. Ya kasance sanannen ɗan siyasa wajen: Ƙarfafa ilimi Tallafa wa matasa Bunƙasa ci gaban karkara Ginin ababen more rayuwa 😢 Martanin jama’a Rasuwarsa ta girgiza al’ummar Jihar Nasarawa da Najeriya baki ɗaya, inda shugabanni, ‘yan siyasa da jama’a suka bayyana mutuwarsa a ma...

Zargin Ta’addanci: Gwamnan Jihar Bauchi Ya Musanta Zarge-zargen da Ake Yi Masa

Image
 An shiga muhawara a kafafen sada zumunta da wasu shafukan intanet biyo bayan zargin da wasu mutane ke yi wa Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, na cewa yana da hannu ko kuma yana goyon bayan ayyukan ta’addanci a wasu sassan ƙasar nan. Zargin ya fara ne bayan wasu maganganu da aka danganta da gwamnan, inda masu suka ke fassara su a matsayin goyon baya ga wasu mutane da ake zargi da aikata laifukan tsaro. Wannan ya jawo ce-ce-ku-ce, musamman daga bangaren ‘yan siyasa da masu sharhi kan harkokin tsaro. Sai dai gwamnatin jihar Bauchi ta fito fili ta musanta dukkan zarge-zargen, tana mai bayyana su a matsayin ƙarya, yaudara da kuma yunkurin ɓata suna domin cimma muradun siyasa. A wata sanarwa daga hadiman gwamnan, an ce: “Gwamnan Bauchi mutum ne mai mutunta doka, kuma yana goyon bayan duk wani mataki da zai kawo ƙarshen ta’addanci da rashin tsaro a Najeriya.” Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnan ya sha yin kira ga gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro da su ƙara ƙaimi wajen magance matsalo...