Kasar Amurka Ta Kama Shugaban Kasar Panama Manuel Noriega
Kasar Amurka Ta Kama Shugaban Kasar Panama Manuel Noriega
A ranar 3 ga Janairu 1990 (yau Shekaru 36 da suka wuce) Manuel Noriega, shugaban kasar Panama, ya mika wuya ga hukumomin Amurka. Kama shi shi ne babban manufar (Operation Just Cause), wata mamayar Amurka mai girma da aka ƙaddamar a kasar a ranar 20 ga Disamba, 1989.
Mamaya bayan hare-haren Jiragen Saman Yaki
Bayan mamayar da sojojin Amurka kimanin 24,000 suka yi, Noriega ya kauce wa kamawa na tsawon kwanaki da dama.
Mafaka a Ofishin Jakadancin Vatican
A ranar Kirsimeti, 1989, Noriega ya nemi mafaka a cikin (ofishin jakadancin Vatican) a birnin Panama.
Domin tilasta masa fita ba tare da karya ka'idojin diflomasiyya ta hanyar shiga ofishin jakadancin ba, sojojin Amurka sun yi amfani wakokin rock da manyan mayan sufiku masu azabar ƙarfi, suka kewaye ofishin jakadancin suka kunna kida ba dare ba rana.
Wasu daga cikin wakokin da suka kunna sun hada da:
Panama" ta Van Halen
"Welcome to the Jungle" ta Guns N' Roses
"I Fought the Law" ta The Clash
"Danger Zone" ta Kenny Loggins
Mika Wuya
Bayan kwanaki 10, Manuel Noriega tare da ma'aikatan ofishin jakadancin basa iya yin barci, dole ta sa Noriega ya fito ya mika wuya ga jami'an Hukumar Kula da Muggan kwayoyi ta Amurka (DEA) a ranar 3 ga Janairu, 1990.
Hukuncin Shari'a
Nan da nan bayan ya mika wuya, an kai Noriega zuwa Miami ta jihar Florida Amurka. A shekarar 1992, an same shi da laifuka takwas na safarar miyagun kwayoyi, damfara, da kuma halatta kudaden haram, wanda hakan ya sanya shi shugaban ƙasa na farko da aka yanke wa hukunci a kotun Amurka.
Hukunci
Da farko an yanke masa hukuncin daurin shekaru 40 a gidan yari (daga baya aka rage shi zuwa shekaru 30). Bayan ya shafe shekaru 17 a Amurka, an mika shi ga Faransa a shekarar 2010 saboda laifin halatta kudaden haram, sannan aka mika shi ga Panama a shekarar 2011 don fuskantar tuhumar kisan kai da cin hanci da rashawa.
Mutuwa
Noriega ya mutu a Asibitin Santo Tomas a birnin Panama a ranar 29 ga watan Mayu 2017 (yana da shekaru 83 ).

Comments
Post a Comment