Shirin Komawa APC: Tijjani Gandu Ya Aika Saƙo Mai Zafi Ga Gwamna Abba Gida-Gida


 Shirin Komawa APC: Tijjani Gandu Ya Aika Saƙo Mai Zafi Ga Gwamna Abba Gida-Gida

Ƙungiyar mawallafan Kwankwasiyya da ke rera wakoki tare da nuna goyon baya ga ƙungiyar Kwankwasiyya da jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ta yi kira ga Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da ya sasanta da Sanata Kwankwaso domin cimma matsaya guda kan makomar magoya bayansu.

Shugaban ƙungiyar mawallafan, kuma fitaccen mawakin Kwankwasiyya da gwamnatin Abba, Tijjani Gandu, ne ya bayyana hakan a wani faifan bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis.

A cewar Tijjani Gandu, sun zaɓi yin bidiyon ne saboda rashin samun damar ganawa kai tsaye da Gwamna Abba Kabir Yusuf. Ya bayyana cewa mawakan Kwankwasiyya na da buƙatar gwamnan ya nemi Sanata Kwankwaso domin su zauna su tattauna, ganin irin doguwar alaƙar siyasa da ke tsakaninsu wadda ta shafe kusan shekaru 40.

Ya ƙara da cewa, a matsayinsu na waɗanda suka taka rawar gani wajen kafa gwamnatin Abba Kabir Yusuf, suna da cikakken haƙƙi na bai wa gwamnan shawara domin a samu daidaito da fahimtar juna.

Tijjani Gandu ya ce Kwankwaso da Abba Kabir Yusuf na iya shiga daki su tattauna cikin lumana, su yanke shawara kan makomar siyasar su, ko komawa kowace jam’iyya da suka ga dama, inda ya jaddada cewa mawakan Kwankwasiyya za su yi biyayya ga duk wata matsaya da aka cimma.

Wannan saƙo na mawakan Kwankwasiyya na zuwa ne a daidai lokacin da ake rade-radin cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na shirin komawa jam’iyyar APC tare da yanke alaƙar siyasa da tsohon maigidan sa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso.

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Yi Tattaunawa da Kwankwaso, Daga Bisani Ya Tafi Faransa Don Ganawa da Tinubu

GWAMNATIN TINUBU TA BIYA ‘DAN LOBBYN REPUBLICAN DALA MILIYAN 9 DON LALLABA TRUMP

SHUGABA TINUBU yaki amincewa da sauya shekar gwamnan kano ba tare da kwankwaso ba