ƊUMI-ƊUMI: Ana fargabar barkewar sabon rikici a Yemen bayan shugaban STC ya ɓac
ƊUMI-ƊUMI: Ana fargabar barkewar sabon rikici a Yemen bayan shugaban STC ya ɓac
e
Ana fargabar barkewar sabon rikici a ƙasar Yemen, bayan rahotanni sun tabbatar da cewa shugaban ƙungiyar Southern Transitional Council (STC), Aidrous al-Zubaidi, ya tsere zuwa wani wuri da ba a bayyana ba.
Kawancen ƙasashen da Saudiyya ke jagoranta ya bayyana cewa al-Zubaidi ya ƙi zuwa Saudiyya domin halartar tattaunawar da aka shirya, wadda ke da nufin kawo ƙarshen rikicin siyasa da na tsaro da ya sake ɓarke a wasu sassan ƙasar.
Mai magana da yawun kawancen, Janar Turki al-Maliki, ya ce an umurci al-Zubaidi da ya shiga jirgin da aka tanada domin ganawa da shugabannin Yemen, amma bai bayyana ba, duk da cewa wasu manyan jami’an STC sun bi umarnin suka tafi Saudiyya.
Bayan kin tafiyar tasa, kawancen ya ce ya gano motsin dakaru da makamai masu nauyi a birnin Aden da kewaye, lamarin da ya haifar da fargabar barkewar rikici tsakanin bangarorin Yemen.
Saboda haka, kawancen ya ce ya ɗauki matakan tsaro na gaggawa, tare da kai hare-haren rigakafi, domin hana rikici da kuma kare fararen hula daga illar yaƙi.
Rahotanni na nuna cewa wannan lamari na iya sake jefa Yemen cikin sabon yanayi na rashin tabbas da tashin hankali.
%20(1).jpeg)
Comments
Post a Comment