ƊUMI-ƊUMI: Isra’ila Ta Kammala Shirye-shiryen Kai Hari Ƙarƙashin Ƙasa Kan Ira

 ƊUMI-ƊUMI: Isra’ila Ta Kammala Shirye-shiryen Kai Hari Ƙarƙashin Ƙasa Kan Ira


n

Rahotanni sun bayyana cewa a ranar Litinin da ta gabata, kwamitin tsaron ƙasar Isra’ila ya amince da shirin ƙaddamar da yaki a kan ƙasar Iran, wani yaki da aka sanya wa suna “Operation Iron Strikes.”

Majiyoyi sun ce an riga an zaɓi rana da lokacin da za a fara kai harin.

Masu nazarin al’amuran tsaro sun yi gargadin cewa idan Isra’ila ta aiwatar da wannan hari, duniya na iya shiga cikin wani mummunan rikici, duba da yadda Iran za ta mayar da martani domin kare kanta.

A shirye-shiryen kare kai, Iran ta fara gwaje-gwajen sabbin makaman linzami masu nisan zango (ballistic missiles), tare da ƙarfafa tsarin tsaron ƙasarta. Wannan mataki ya ƙara tayar da hankalin Isra’ila da kawayenta, musamman Amurka.

Rahotanni sun nuna cewa Isra’ila da Amurka na fatan rusa tsarin mulkin Iran domin kafa shugabancin da zai yi musu biyayya. A halin yanzu, ana kallon Iran a matsayin ɗaya daga cikin ƙasashen da Isra’ila ke fi tsoro, sakamakon ƙarfin makaman da take mallaka.

Tsawon shekaru, an kakaba wa Iran takunkuman tattalin arziki masu tsauri domin raunana ƙasarta. Sai dai duk da hakan, Iran ta ƙi durƙusawa, maimakon haka tana ƙara ƙarfi wajen ƙera sabbin makamai masu linzami da kuma haɓaka shirin makamin nukiliyarta.

Gwaje-gwajen makaman da Iran ta gudanar a kwanakin nan sun ƙara tabbatar wa Isra’ila cewa harin da ta kai a bara bai lalata cibiyoyin ƙera makaman linzami na Iran ba. Wannan na daga cikin manyan dalilan da suka sa Isra’ila ke shirin sake kai mata hari a wannan lokaci.

Comments

Popular posts from this blog

Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Yi Tattaunawa da Kwankwaso, Daga Bisani Ya Tafi Faransa Don Ganawa da Tinubu

GWAMNATIN TINUBU TA BIYA ‘DAN LOBBYN REPUBLICAN DALA MILIYAN 9 DON LALLABA TRUMP

SHUGABA TINUBU yaki amincewa da sauya shekar gwamnan kano ba tare da kwankwaso ba