ƊUMI-ƊUMI: Jirgin tsaron gabar tekun Amurka na bin jirgin dakon mai mai tutar Rasha a tekun Atlantika

 Jirgin ruwan tsaron gabar tekun Amurka na ci gaba da bin diddigin wani jirgin dakon man fetur mai dauke da tutar Rasha a yankin arewacin tekun Atlantika, bayan da ake zargin jirgin ya keta shingen tsaro da Amurka ta kafa a yankin.

Rahotanni sun bayyana cewa jirgin dakon man na Rasha ne, kuma har yanzu bai tsaya ba duk da kokarin da sojojin ruwan Amurka ke yi na tilasta masa tsayawa.

Sai dai sojojin Amurka sun jaddada cewa burinsu shi ne kwace jirgin dakon man, ba wai kai masa hari ko haddasa nutsewarsa ba.

Amurka na zargin cewa jirgin yana jigilar man fetur ne daga kasashen Iran da Venezuela, lamarin da ta ce ya saba wa takunkumin tattalin arziki da ta kakabawa kasashen


Comments

Popular posts from this blog

Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Yi Tattaunawa da Kwankwaso, Daga Bisani Ya Tafi Faransa Don Ganawa da Tinubu

GWAMNATIN TINUBU TA BIYA ‘DAN LOBBYN REPUBLICAN DALA MILIYAN 9 DON LALLABA TRUMP

SHUGABA TINUBU yaki amincewa da sauya shekar gwamnan kano ba tare da kwankwaso ba