Yan Ta’adda Sun Kashe Mutum 7 a Sabon Hari a Filato
Aƙalla mutane bakwai ne suka rasa rayukansu sakamakon wani sabon harin dare da wasu ‘yan ta’adda suka kai a garin Bum, da ke cikin ƙaramar hukumar Vwang (Vwamg) a Jihar Filato.
Rahotanni sun nuna cewa maharan sun shiga garin ne cikin dare, inda suka rika harbe-harbe ba kakkautawa, lamarin da ya jefa al’ummar yankin cikin fargaba da tashin hankali. Mutanen da abin ya shafa sun hada da mazauna garin da ba su ji ba su gani ba.
Wasu mazauna yankin sun ce bayan harin, an gano gawarwakin mutane bakwai, yayin da ake fargabar cewa adadin na iya ƙaruwa saboda wasu sun jikkata kuma ana ci gaba da neman wasu da suka bace.
Har zuwa lokacin hada wannan labari, hukumomin tsaro ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba, sai dai an ce an tura jami’an tsaro zuwa yankin domin dawo da zaman lafiya da kuma gudanar da bincike.
Al’ummar garin Bum sun bukaci gwamnati da hukumomin tsaro da su dauki matakan gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a, ganin yadda hare-haren ke kara yawaita a wasu sassan Jihar Filato.

Comments
Post a Comment