Zamu karbi Greenland koda tsiya tsiya cewar Donald Trump
Yayin da yake jawabi ga manema labarai a ranar Juma’a, Mista Donald Trump ya bayyana cewa wasu ƙasashe na nuna sha’awar mallakar yankin Greenland, yana mai cewa “dole ne Amurka ta ɗauki matakan kare aukuwar hakan.”
A kwanakin baya, Fadar White House ta tabbatar da cewa tana nazarin yiwuwar sayen yankin daga ƙasar Denmark. Sai dai, duk da wannan mataki, ta jaddada cewa har yanzu ba a kawar da yiwuwar amfani da ƙarfin soji domin mamaye yankin ba.
Sai dai wannan furuci ya fuskanci martani mai ƙarfi daga Denmark da kuma hukumomin tsibirin Greenland, inda suka bayyana karara cewa yankin ba na sayarwa ba ne, kuma ba za su amince da kowace irin mamaya ba.
A halin yanzu, tsibirin Greenland na ci gaba da jan hankalin manyan ƙasashen duniya, sakamakon dumbin albarkatun ma’adinai da ke ɓoye a ƙarƙashin ƙankarar yankin, lamarin da ke ƙara tsananta fafatawar siyasa da tattalin arziki a yankin Arctic.
.jpeg)
Comments
Post a Comment